Koma Labarai
Lafiya

Gwamnan Kano ya ƙaddamar da rabon takardun ɗaukar aiki ga ma'aikatan lafiya sama da dubu biyu

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Gwamnan Kano ya ƙaddamar da rabon takardun ɗaukar aiki ga ma'aikatan lafiya sama da dubu biyu

‎Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da rabon takardun ɗaukar aiki na din-din-din ga ma'aikatan Lafiya dubu biyu da dari bakwai daga ƙananan hukumomi 44 na jihar.

Gwamnan ya miƙa takardun ɗaukar aikin ne a ɗakin taro na Coronation da ke gidan gwamnatin Kano, a ranar Laraba 30 ga watan Satumban 2026.

‎Abba Kabir ya ce gwamnatinsa ta baiwa bangaren kiwo lafiya muhimmancin da cigaba da kula da lafiya tun daga matakin farko, tare da gyaran asibitocin gwamnatin a fadin jihar Kano.

‎A cewar gwamnan, ya zama wajibi gwamnati ta baiwa ɓangaren kiwon lafiya kulawa tare da samar da ma'aikatan Lafiya, domin kula da lafiya al'ummar jihar Kano.

Yusuf ya ƙara da cewar gwamnatinsa ta dauki matasa Maza da Mata dubu biyu da dari bakwai da talatin da bakwai aikin a bangare kiwon lafiya, domin kula da kiwon lafiyar al'ummar jihar.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM