Gwamnatin Kano ta fara rigakafin cutar mashako a ƙananan hukumomi biyar na jihar.

Gwamnatin Jihar Kano ta fara gudanar da shirin rigakafin cutar mashako a kananan hukumomi biyar domin dakile yaduwar cutar.
Kananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗar da Dala, da Fagge, da Gwale, da kuma Kumbotso da Ungoggo, inda ake gudanar da aikin a unguwanni 13.
Cibiyar Kula da yaɗuwar Cututtuka ta jihar Kano (KNCDC) ta ce shirin ya shafi unguwannin Gobirawa, Kofar Ruwa, Kwachiri, Rijiyar Lemo, da kuma Ɗorayi, da Kabuga, sai Chiranchi, da Naibawa, da kuma Fanshekara, da Bachirawa, Gayawa, Rijiyar Zaki da kuma Ungoggo.
Cibiyar ta bukaci mutanen da ba su san matsayin rigakafinsu ba, ko kuma waɗanda suka kwashe sama da shekaru 10 ba tare da karɓar allurar ba, da su je cibiyoyin da aka ware domin yin rigakafin.
Hukumar ta KNCDC ta bayyana cewa, rigakafin na da aminci kuma yana taimakawa wajen kare mutane daga kamuwa da cutar Diphtheria.
A watan Agustan 2026 ne gwamnatin Kano ta nemi gwamnatin tarayya da ta samar mata da karin alluran rigakafin cutar domin gudanar da gangamin rigakafi a fadin jihar.



