Koma Labarai
Lafiya

Ƙungiyar masu "Chemist" ta jihar Kano, ta yi barazanar tsunduma yajin aikin gargaɗi.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Ƙungiyar masu "Chemist" ta jihar Kano, ta yi barazanar tsunduma yajin aikin gargaɗi.

Ƙungiyar masu "Chemist" ta jihar Kano, ta yi barazanar tsunduma yajin aikin gargaɗi, matuƙar ƙungiyar lmasu haɗa magunguna (PCN) ba ta daina matsa musu lamba ba.

Shugaban ƙungiyar masu "Chemist" din na jihar Kano Kwamared Aminu Hikima, ne ya bayyana hakan a zantawarsa da gidan rediyon Dala FM Kano, a ranar Litinin 7 ga watan Satumba, 2026.

Wakilinmu Abubakar Sabo ya ruwaito cewa, Kwamared Aminu ya kuma buƙaci gwamnatin jihar Kano, da ta shiga cikin lamarin domin kawo ƙarshen ƙalubalen da suke fuskanta daga ƙungiyar ta PCN.

Ready to PlayDala FM88.5 FM