Koma Labarai
Lafiya

Gwamnatin jihar Kano ta buƙaci limamai su wayar da kan jama'a kan muhimmancin yin katin zaɓe

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Gwamnatin jihar Kano ta buƙaci limamai su wayar da kan jama'a kan muhimmancin yin katin zaɓe

Gwamnatin jihar Kano ta buƙaci al'umma da su tashi tsaye wajen zuwa a yi musu katin zaɓe, tana mai cewa suma masu gyara a katin nasu su je a gyara musu, bisa mahimmancin sa a rayuwar su, da ma tabbatar da ƴancin su.

Kwamishinan yaɗa labarai da al'amuran cikin gida na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya, ne ya bayyana hakan, a yayin taron da Karamin Kwamitin limamai, na babban kwamitin Karta-kwana a kan katin zaɓe da gwamnatin jihar Kano ta kafa ya gudanar, domin wayar da kan limamai kan muhimmancin yin katin zaɓe don tabbatar da ƴancin su.

Kwamishinan, da ya samu wakilcin Kwamared Abbas Ibrahim, Shugaban ƙaramin Kwamitin Ƙwadago, a Kwamitin Karta-kwana a kan katin zaben, ya buƙaci al'umma da su tabbata an yi musu katin zaɓe domin tabbatar da ƴancin su tare da zaɓar nagarta a yayin zaɓen 2027.

Da yake nasa jawabin, Shugaban Ƙaramin Kwamitin limamai, kuma Sakataren Majalisar limamai ta ƙasa reshen jihar Kano, Mallam Ibrahim Abubakar Tofa, ya ce taron ya mayar da hankali ne a kan wayar da kan limamai kan su yi kira ga al'umma musamman ma a huɗubobin su, mahimmancin yin katin zaɓe.

Shima a nasa ɓangaren, Kwamishina na biyu a hukumar Shari'a ta jihar Kano, kuma guda daga cikin ƴan Ƙaramin Kwamitin limaman a kan katin zaɓen, Sheikh Ali Ɗanabba, buƙatar jama'a da ma iyaye ya yi, da su tabbata ƴaƴansu sun mallaki katin zaben bisa mahimmancin sa a rayuwar su ta ɓangarori daban-daban.

Dala FM Kano ta ruwaito cewa taron da ya gudana ne yau Alhamis, a ɗakin taro na Ɗakin Karatu na jihar Kano, inda ya samu halartar Limaman masallatan Juma'a da na Kamsul-Salawati, da manyan baƙi da dama, kuma ciki har da Malami a sashin koyar da harkokin siyasa a Jami'ar Bayero da ke nan Kano, Farfesa Kamilu Sani Fagege, da Dr. Abdussalam Sheikh Nasiru Kabara, da sauransu.

Ready to PlayDala FM88.5 FM