Babban burina yanzu na fi kowa kuɗi a duniya - Aliko Ɗangote
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Fitaccen attajirin Najeriya, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa babban burinsa a yanzu shi ne ya kamo attajirin Amurka, Elon Musk, ta fuskar arziki, yana mai cewa ba zai damu ba idan wani ɗan Najeriya ya zarce shi a kuɗi.
Dangote ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai a matatar mansa da ke Legas, inda ya ce yana fatan ganin ’yan Najeriya sun ƙara samun wadata tare da samun waɗanda za su zarce shi a arziki.



