Koma Labarai
Tattalin Arziki

Sarkin Kano Sanusi ya gana da jami’an Hong Kong kan bunƙasa alaƙar tattalin arziƙi da Najeriya

Hassan Mamuda Ya'u 32 views
Sarkin Kano Sanusi ya gana da jami’an Hong Kong kan bunƙasa alaƙar tattalin arziƙi da Najeriya

Mai martaba Sarkin Kano, Khalifa Dr. Muhammadu Sanusi II, ya gana da jami’an Gwamnatin Hong Kong domin tattauna hanyoyin ƙarfafa alaƙar tattalin arziki tsakanin Hong Kong da Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa an gudanar da taron ganawar ne a ranar Juma’a, 23 ga Oktoba, 2026.

An gudanar da taron ne ƙarƙashin jagorancin Mr. Joseph H. L. Chan, JP, Mataimakin Sakatare mai kula da Ayyukan Kuɗi da Baitulmalin Gwamnatin Hong Kong Special Administrative Region (HKSAR).

An gayyaci Mai Martaba Sarkin ne bayan jami’an gwamnatin sun samu labarin cewa yana ƙasar, inda aka nemi shawarwarinsa kan hanyoyin inganta haɗin gwiwar tattalin arzikin ƙasashen biyu.

Mai Martaba Sarkin ya samu rakiyar Galadiman Kano, Alhaji Munir Sanusi.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM