Hauhawar farashi ya ragu a Nijeriya da kaso 14.63 cikin 100 a watan Satumban 2026 - NBS
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Rahotanni sun bayyana cewa Hukumar kididdiga ta Nijeriya NBS ta ce, hauhawar farashin kayayyaki a kasar ya ragu zuwa kashi 14.63 cikin 100 a watan Satumba na shekarar 2026, daga kashi 15.39 cikin 100 da aka samu a watan Agusta.
Hukumar ta NBS ta bayyana hakan ne a cikin rahotonta na ma’aunin farashin kayayyakin masarufi (Consumer Price Index), wanda ta fitar a ranar Alhamis, inda ta nuna cewa, an samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya a watan da ake nazari, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Rahoton ya kuma nuna cewa, hauhawar farashin kayayyaki ta ragu da maki 6.35 bisa ɗari idan aka kwatanta da kashi 20.98 cikin 100 da aka samu a watan Satumba na shekarar 2025.

