Koma Labarai
Labarai

Masu filaye da gonaki a Kuyan ta Inna sun fito zanga-zanga a kan neman diyyar kadarorin su

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Masu filaye da gonaki a Kuyan ta Inna sun fito zanga-zanga a kan neman diyyar kadarorin su

Mamallaka filaye da gonaki a yankin Kuyan ta Inna da ke ƙaramar hukumar Kumbotso a Kano, sun yi dafifi domin gudanar da zanga-zangar lumana kan yadda aka gaza biyan su diyyar kadarorin su da aikin gwamnatin tarayya ya biyo ta ciki, amma aka ci gaba da baje musu gurare a safiyar nan.

Masu guraren sun ce an haura shekaru biyu ana dambarwa a kan batun biyansu kuɗaɗen kadarorin su, har kotu ta yi hukunci kan cewar ba za a ci gaba da aikin baje guraren nasu ba, da aikin "Dry Port" ya biyo ta ciki, har sai an biya su diyya, sai gashi ba a biya su ba amma an ci gaba da aikin.

Sun ƙara da cewa, aƙalla sun haura su 75 waɗanda aikin ya biyo ta filaye da gonakin su, waɗanda kawo yanzu babu wanda aka biya diyya, a don haka ne su ke neman ɗaukin dukkanin masu ruwa da tsaki da su kawo musu agaji wajen ganin an biya su diyyar kadarorin su.

Mu na tafe da ƙarin bayani...

Ready to PlayDala FM88.5 FM