Koma Labarai
Labarai

Rashin al'amuran more rayuwa na damun yankunan mu - Mazauna Batakaye da kewaye

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Rashin al'amuran more rayuwa na damun yankunan mu - Mazauna Batakaye da kewaye

Al'ummar unguwannin Ɗanmaliki, Batakaye, Bechi, da kewaye da ke ƙaramar hukumar Kumbotso a Kano, sun nemi shugaban ƙaramar hukumar su Ali Musa Ɗanmaliki (Hardwoker), da ya magance musu matsalalolin rashin hanya, da wutar lantarki, da ruwan Famfo, da kuma samar musu asibiti domin samun sauƙi a rayuwar su.

Guda daga cikin mazauna yankin Sani Isah Batakaye, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM Kano, yana mai cewa duba da yadda suke fuskantar ƙalubale a kan rashin al'amuran more rayuwa a yankin nasu akwai buƙatar a kai musu ɗauki.

Ya kuma yi kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki da su kai musu ɗauki domin ganin an magance wa al'ummar yankin Batakaye, da Bechi, da Ɗanmaliki, da kewaye Matsalolin da suke damunsu na ƙarancin al'amuran more rayuwa, domin su san ana gwamnati.

A cewar sa, "Tun lokacin da shugaban ƙaramar hukumar mu Hon. Ali Musa Hardwoker, yake Kansila, mu ke ta ƙoƙari wajen ganin an kawo ci gaba a yankunan mu, dama ya san da matsalolin kuma mu na fatan zai shige mana gaba domin ganin an magance su, in ji shi.”

Sani Isah ya kuma ce sun shafe tsawon wasu shekaru suna fama da waɗannan matsaloli al'amarin da ke matuƙar ci musu tuwo a ƙwarya.

Ready to PlayDala FM88.5 FM