Koma Labarai
Labarai

Gwamnan Kano zai biya ƴan fansho naira Biliyan biyar a jihar

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Gwamnan Kano zai biya ƴan fansho naira Biliyan biyar a jihar

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, zai sake biyan 'yan fansho naira biliyan biyar, domin biyan su haƙƙoƙin su.

Dala FM Kano ta ruwaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Babban Daraktan yaɗa labaran gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar yau a shafinsa na Facebook.

Ya kuma ce biyan ƴan fanshon da Gwamna Abba Abba Kabir Yusuf, zai yi zai kasance karo na shida ke nan yana biyan su haƙƙoƙin nasu.

Ready to PlayDala FM88.5 FM