Koma Labarai
Labarai

Ƙaramar Hukumar Fagge ta yi Allah wa-dai da kalaman wani mutum a kan Sheikh Umar Sani Fagge

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Ƙaramar Hukumar Fagge ta yi Allah wa-dai da kalaman wani mutum a kan Sheikh Umar Sani Fagge

Shugaban ƙaramar hukumar Fagge Hon. Salisu Usman Masu, ya bayyana fitaccen malamin addinin Musuluncin nan Sheikh Umar Sani Fagge, a matsayin babban jigo a harkar addini a jihar Kano, da Arewa, da ma ƙasa gaba ɗaya.

Hon. Masu, ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a ranar Litinin 30 ga watan Maris, 2026, lokacin da yake martani a kan kalaman wani mutum a kan malamin.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da wani mazauni Arewacin ƙaramar hukumar Fagge, ya yi wasu kalamai na ɓatanci a kan Sheikh Umar Sani Fagge, lamarin da Hon. Masu ya yi Alla-wadai da waccan magana.

Hon. Salisu Masu ya kuma bayyana cewar, da arewacin ƙaramar hukumar Fagge da cikin fagge duk abu ɗaya ne babu banbanci.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, daga ƙarshe Masu ya kuma baiwa malamin da ma almajiransa hakuri kan faruwar lamarin.

Ready to PlayDala FM88.5 FM