Wutar lantarki za ta inganta nan ba da jimawa ba a Najeriya - Shugaba Tinubu
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa gwamnatinsa na ɗaukar matakai masu ƙarfi domin magance matsalar rashin wutar lantarki da ake fama da ita ƙasar.
Shugaba Tinubi ya bayyana hakan ne yayin babban taron jam’iyyar APC da aka gudanar jiya Juma'a, a Eagle Square da ke Abuja, inda ya amsa korafe-korafen jama’a kan yawan katsewar wutar lantarki a ƙasar.
A cewar sa, "Gwamnati na mayar da hankali sosai kan matsalar, tare da ɗaukar matakai domin inganta wutar lantarki a watanni masu zuwa, in ji Tinubu.”
Kazalika, ya kuma bayyana cewa kamfanin kula da layin wutar lantarki, zai ƙara samar da wuta mai ƙarfin megawatt 1,500 domin ƙarfafa rarraba wutar, kamar yadda DCL Hausa ta ruwaito.



