Koma Labarai
Labarai

An haifi jarirai sama da 36,000, cikin watanni tara kacal a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
An haifi jarirai sama da 36,000, cikin watanni tara kacal a Kano

Hukumar Ƙidaya ta ƙasa, National Population Commission, ta bayyana cewa an yi rijistar haihuwar jarirai sama da 36,000 a Jihar Kano cikin watanni tara kacal.

Daraktan hukumar a Kano, Balarabe Kabir, ne ya bayyana hakan yayin wani taron horas da masu horaswa da aka gudanar a jihar.

Ya ce nasarar ta biyo bayan fara amfani da tsarin rijistar haihuwa ta na’ura, wanda ya sauƙaƙa tattara bayanan yara cikin sauri da inganci.

A cewarsa, an gudanar da taron ne tare da haɗin gwiwa da "Nigerian Union of Local Government Employees" da kuma "National Identity Management Commission", tare da tallafin ƙasashen waje da kuma UNICEF.

Hukumar ta kuma bayyana cewa an tantance kusan yara 27,000 ‘yan ƙasa da shekaru biyar, da kuma sama da 40,000 da suka haura wannan shekaru, waɗanda ba a taɓa yin rijistar su ba a baya, a wani yunƙuri na tabbatar da cewa kowane yaro yana da rajista a hukumance.

Ready to PlayDala FM88.5 FM