Shugaba Tinubu ya taya Musulmi murnar Sallah, tare da kira zuwa ga kishin ƙasa

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya al’ummar Musulmi murnar ƙaramar Sallah, (Eid-el-Fitr), tare da kira ga al'umma da su ƙara jajircewa wajen hidimtawa ƙasa da jama'a baki ɗaya.
Tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewa, wannan na cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban ƙasar shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis 19 ga watan Maris, 2026.
Shugaban ya kuma bukaci Musulmi su ci gaba da riƙe darussan watan Ramadan, musamman waɗanda suka shafi tsoron Allah, tausayi da haɗin kai tsakanin al’umma.
Ya ce akwai darussa masu yawa da ya kamata a ɗauka daga Ramadan, musamman a irin wannan lokaci, yana mai jaddada muhimmancin bin kyawawan halaye kamar sadaukarwa, juriya, alheri da jin ƙai har bayan watan azumi.
Shugaba Tinubu ya kuma buƙaci Musulmi da su miƙa taimako ga masu buƙata ba tare da la’akari da addini ba, domin ƙarfafa zumunci da haɗin kai a tsakanin ‘yan ƙasar.
Haka zalika, ya roƙi shugabannin addini da su yi amfani da wannan lokaci wajen yi wa ƙasa addu’o’in zaman lafiya da ci gaba.
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnatin za ta ci gaba da ƙoƙarin samar da yanayi mai kyau domin walwalar al’umma.



