Koma Labarai
Labarai

Ramadan: Ƙungiyar Darussa'adah Islamic ta tallafa wa marayu 100, kayan sallah da na abinci a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Ramadan: Ƙungiyar Darussa'adah Islamic ta tallafa wa marayu 100, kayan sallah da na abinci a Kano

Dagacin garin Ja'oji da ke ƙaramar hukumar Kumbotso a Kano, Alhaji Sule Shuaibu, ya ce akwai buƙatar mawadata su rinƙa ɗaukar nauyin marayu kamar abinda ya shafi ci da shan su, da kuma karatunsu, domin rage musu wani raɗaɗi bisa rasuwar mahaifinsu.

Dagacin ya bayyana hakan ne ta hannun wakilcin da ya samu na Alhaji Nura Shu'aibu, a yayin taron da ƙungiyar tallafa wa marayu ta Darussa'adah Islamic Orphans, ta gudanar yau domin rabawa marayu kayan sallah da kuma kayan abinci ga iyayensu aƙalla su 100 a Sabuwar Mandawari da ke Kano.

Da yake nasa jawabin Uba a kungiyar ta Daruss'ada, Malam Ɗalhatu Adamu, ya ce bana an sami gagarumar nasara da ta fi ta bara inda aka sami tallafa wa marayu su ɗari 100, domin taimaka wa rayuwar su.

Shima a nasa ɓangaren, shugaban ƙungiyar ta Darussa'adah Islamic Orphans a Kano, Kwamared Musa Nasiru Musa, ya ce a bana mawadatan yankin da ma na sassan Kano, sun yi abin a yaba ganin yadda suka bada gudummawa ga ƙungiyar don taimaka wa marayun.

A cewar sa, "Za mu ci gaba da ƙoƙari wajen tallafa wa marayu ta ɓangarori daban-daban domin inganta rayuwar tare da rage musu wani raɗaɗin rayuwa, in ji Musa.”

Wakilinmu Nasir Khalid Abubakar da ya halarci taron ya rawaito cewa, al'umma da dama ne suka halarci taron rabon tallafin, kuma cikin har da limaman yankin da dama.

Ready to PlayDala FM88.5 FM