Koma Labarai
Labarai

Kashi 82 bisa 100 na 'yan Najeriya ba sa koshi a mulkin Tinubu - Jam'iyyar ADC

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Kashi 82 bisa 100 na 'yan Najeriya ba sa koshi a  mulkin Tinubu - Jam'iyyar ADC

Rahotanni sun bayyana cewa jam’iyyar adawa ta ADC ta mayar da martani ga APC, kan kare manufofin tattalin arzikin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, inda ta ce ‘yan Najeriya suna cikin uƙuba a mulkin Tinubu.

Wannan na cikin sanarwar da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar ADC na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya sanya wa hannu.

Kazalika, ADC ta kuma musanta zargin cewa tana tunzura ‘yan ƙasa, tana mai cewa rahotannin da ke nuna ƙaruwar talauci zuwa kashi 63 cikin ɗari ba maganar siyasa ba ce, illa sakamakon bincike da ke nuna halin da jama’a ke ciki a Najeriya.

Har ila yau, ADC ta ce kafin cire tallafin man fetur, talauci a Najeriya na tsakanin kashi 50 bisa ɗari, amma yanzu ya ƙaru zuwa kashi 63, lamarin da ta ce ya jefa miliyoyin mutane cikin ƙuncin rayuwa a ƙasar.

"Bayanai sun nuna cewa kashi 82 na ‘yan Najeriya sun taɓa rasa isasshen abinci a cikin shekarar da ta gabata, kashi 82 ba su samu kulawar lafiya ba, kashi 79 ba su samu man girki ba, yayin da kashi 74 suka rasa ruwan sha mai tsafta a sassan ƙasar"

Ready to PlayDala FM88.5 FM