Ramadan: Ƙungiyar Matasa Musulmi ta bada tallafin kayan sallah da na abinci ga yara marayu da iyayensu su 150 a Kano.

Ƙungiyar Matasa Musulmi ta jihar Kano, KAMYA, ta ƙaddamar da bada tallafin kayan sallah da na abinci ga yara marayu da iyayen su 50, a babban ofishin ta da ke ƙaramar hukumar Gwale a Kano, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa.
Shugaban ƙungiyar ta Kano State Muslim Youth Association (KAMYA) Kwamared Imam Muntaƙa Abdulmalik, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM Kano, a ranar Alhamis 12 ga Maris, 2026.
Ya ce sun gudanar da taron rabon kayan abinci da kuma na sallah, ga marayu da iyayen nasu 50, ne a ranar Laraba 11 ga watan Maris, 2026, a babban ofishin ƙungiyar da ke yankin Ja'en a ƙaramar hukumar Gwale a Kano.
Kwamared Imam Muntaƙa, ya kuma ce ƙungiyar tasu ta KAMYA, reshen ƙaramar hukumar Kabo, ta bada tallafin kayan sallar da kuma kayan abinci, ga yara marayu da iyayen su, domin sanya farin ciki a zukatan su a cikin wannan wata na Ramadana.
A cewar sa, “Cikin kayan sallar da mu ka raba wa marayu karo na biyar, sun haɗar da Atamfofi, da Yadiddika ga yara marayu, kuma a shirye mu ke wajen ci gaba da tallafa musu domin suma su gudanar da bikin sallah kamar masu iyaye, in ji shi.”
Imam Muntaƙa, ya kuma yi kira ga masu hali, da ma ƴan ƙungiyoyin ci gaban al'umma, da su ƙara haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen tallafa wa yara marayu waɗanda iyayensu suka rasu, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa.



