Koma Labarai
Labarai

Yajin aiki: Ƙungiyar lauyoyin gwamnatin Kano ta kulle ƙofar shiga babbar kotun Sakatariyar Audu Baƙo

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Yajin aiki: Ƙungiyar lauyoyin gwamnatin Kano ta kulle ƙofar shiga babbar kotun Sakatariyar Audu Baƙo

An kulle ƙofar shiga babbar kotun jihar Kano, da ke sakateriyar Audu Baƙo, sakamakon yajin aikin sai baba ta gani da ƙungiyar lauyoyin gwamnatin jahar suka tsunduma.

Lauyoyin gwamnatin Kano, sun tsunduma yajin aikin ne da safiyar yau Laraba 11 ga Maris, 2026, sakamakon rashin biyan su wasu haƙƙoƙinsu da suka ce doka ce ta yi tanadin a biya su.

Tuni dai Hukumar gudanarwa ta ma'aikatar shari'a ta jihar Kano, ta bayyana cewar za a hukunta duk lauyan da bai fito aiki a yau Laraba ba.

Hukumar gudanarwar ta bayyana cewar tun daga kan daraktoci har zuwa kan ƙananun ma'aikata ba a ɗauke wa kowa zuwa aiki ba.

Wakilin Dala FM Kano, Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, hukumar ta kuma ce bijirewa sanarwar dai-dai ta ke da saɓawa dokar ɗauka da ladabtar da ma'akaci.

Ready to PlayDala FM88.5 FM