Koma Labarai
Labarai

Mu na ƙokari tuƙuru wajen biyan lauyoyin gwamnatin Kano haƙƙoƙin su - Ma'aikatar Shari'a

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Mu na ƙokari tuƙuru wajen biyan lauyoyin gwamnatin Kano haƙƙoƙin su - Ma'aikatar Shari'a

Ma'aikatar Shari'a ta jihar Kano, ta bayyana cewar tana ƙoƙari domin ganin ana biyan lauyoyin gwamnatin jihar haƙƙoƙinsu kamar yadda doka ta danadar.

Tashar Dala FM Kano, ta ruwaito cewa wannan na cikin ƙunshin wata sanarwa da ma'aikatar shari'ar ta fitar a ranar Talata 10 ga watan Maris, 2026, a Kano.

Kwamishinan ma'aikatar shari'ar ta Kano, Barrister Abdulkarim Maude SAN, ya kuma roƙi ƙungiyar lauyoyin gwamnati da su yi wa mahukuntan ma'aikar hanzari tare da ci gaba da bayar da hadin kai da aiki tuƙuru.

A cewar sa, "Ma'aikatar na yin aiki tuƙuru domin kyautata yanayin aiki cikin kyakkyawan tsari sannan ana yin aiki tuƙuru dangane da haƙƙoƙin lauyoyin gwamnatin Kano, in ji Maude.”

Ma'aikatar shari'ar ta kuma buƙaci ma'aikatan ta da su fito aiki a gobe Laraba 11 ga watan Maris, 2026, domin ci gaba da gudanar da aiki.

Wakilinmu Yusif Nadabo ya rawaito cewa, hakan na zuwa ne a dai-dai lokacin da ƙungiyar lauyoyin gwamnati reshen jahar Kano, ke barazanar tafiya yajin aikin sai baba ta gani sakamakon jan ƙafa a kan haƙƙoƙinsu da su ke maƙalewa.

Ready to PlayDala FM88.5 FM