Ramadan: Ku ruɓanya taimaka wa masu ƙaramin don rage musu raɗaɗin rayuwa - Human Rights

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam da ba da agaji ta Center for Human Rights and Charity Development initiatives, ta buƙaci masu hali da su ruɓanya taimaka wa masu ƙaramin ƙarfi a wannan lokaci na watan azumin Ramadan, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa.
Babban Daraktan ƙungiyar a Najeriya, Kwamared Dr. Auwal Jibril Maifada, ne ya buƙaci hakan a yayin taron shan ruwan da ƙungiyar ta gudanar ranar Juma'a 6 ga watan Maris, 2026, a babban ofishin ta da Kano.
Ya ce duba da yanayin tsadar rayuwar da al'umma suka samu kansu yanzu a ciki a sassan ƙasar, akwai buƙatar Gwamnati, da masu hali, su tashi tsaye wajen tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi don ƙara inganta rayuwar su.
A cewar sa, "Mun shirya taron shan ruwan da ƴan ƙungiyar mu, da ma sauran al'umma domin faranta wa juna rai, tare da rabauta da ladan da Allah S.W.T, yake bayar wa a cikin wannan wata na Ramadan; kuma zamu faɗaɗa shan ruwan a sassan jahohin Najeriya, a duk lokacin Azumin na Ramadan, in ji Dr. Auwal.”
Ya kuma ce a yayin taron shan ruwan an sada zumunci, tare da lalubo hanyoyin ƙara bada agaji musamman ma ta hanyar ciyar wa da sauransu, a tsakanin talaka wa domin sanya musu farin ciki, duba da halin ƙuncin rayuwar da aka samu kai a ciki a ƙasar.



