Za a gurfanar da duk wanda yaci mutuncin gwamnan Kano, ko wani mutum a kotu - Gwamnatin Kano

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewar za ta gurfanar da duk wani mutum da aka kama da laifin cin mutuncin mutane, a dai-dai lokacin da wasu matasa su ke yi wa gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ɗan kira.
Kwamishinan shari'a na jihar Kano, Barrister Abdulkarim Maude SAN, ne ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai da ya gudana a ranar Juma'a ma'aikatar sharia ta jihar Kano.
Kwamishinan ya bayyana cewar doka ta yarda da faɗin albarkacin baki amma ba ta yadda da cin mutunci ba.
A cewar sa, "Za mu gurfanar da duk wani mutum da masu bincike suka samu da laifi a kan sa a gaban kotu, in ji shi.”
Wakilinmu Yusif Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, jawabin kwamishinan na zuwa ne dai-dai lokacin da wasu matasa suke yi wa gwamnan kano ɗan kira a kan hanya.
