Kisan Kabara: Kwamishinan Ƴan Sanda, da Gwamnatin Kano a bi mana jinin ƴan uwan mu - Ƙungiyar KSCEDA
Ƙungiyar haɗin kan unguwar Kabara don Ilimi, da tsaro da ci gaban Al’umma, ta (KCSEDA) ta ɗauki matakin shigar da ƙorafin ta a rubuce ga kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, kan buƙatar a zurfafa bincike game da harbin ƴan unguwar su huɗu da wasu jami'an tsaro suka yi har ɗaya ya rasu a kwanakin baya.
Jami'in hulɗa da jama'a na ƙungiyar ta Community Security, Education and Development Association (KCSEDA) Haruna Salisu Sa'adu, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da Dala FM Kano, a ranar Lahadi 22 ga watan Fabrairu, 2026, a Kano.
A cewar sa, "Ƙungiyar mu ta yi haɗin gwiwa ne da ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Rights Network, wajen shigar da ƙorafin zuwa ga ofishin Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, domin ganin ya gudanar da bincike tare da ɗaukar matakin da ya dace a kan lamarin harbin don gujewa aukuwar irin hakan a gaba, in ji shi.”
Ya kuma ƙara da cewa, a kwanakin baya ne wasu jami'an tsaro su ka je yankin na Kabara, domin kwantar da tarzoma game da yadda wasu ɓata gari su ka shiga yankin, sai dai jami'an tsaron su ka saki kunamar bindigar su a kan ƴan ba ruwana, ƴan unguwar su huɗu, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwar guda daga cikin matasan yankin.
Haruna Salisu Kabara, ya kuma yi kira ga Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, da Gwamnatin jihar Kano, da dukkanin masu ruwa da tsaki, da su shiga cikin lamarin don ganin an gaggauta ɗaukar matakin da ya dace kan lamarin, tare da fitar wa matasa hakƙin su.
Da yake nasa jawabin, Babban daraktan ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Rights Network, a Najeriya, Ambasada Ƙaribu Yahaya Lawan Kabara, ya ce ba za su bari haƙƙin matasan ya ta fi a banza ba, a don haka za su yi duk mai yi yuwa domin ganin an yi adalci a kan lamarin.
Ya kuma ce, ƙungiyar tasu za ta ci gaba da haɗin gwiwa da ƙungiyar ta KCSEDA, wajen bibiyar al'amarin a duk inda ya dace, domin ganin an gaggauta yin bincike tare da ɗaukar matakin da ya dace a kan duk jami'in tsaron da aka samu da hannu a aika-aikar, domin daƙile faruwar irin hakan a gaba.
