Koma Labarai
Labarai

Majalisa ta amince da kafa dokar hukumar ɗaukar ma'aikatan ƙananan hukumomi a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Majalisa ta amince da kafa dokar hukumar ɗaukar ma'aikatan ƙananan hukumomi a Kano.

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kafa dokar hukumar ɗaukar ma'aikatan ƙananan hukumomi, da za ta basu damar ɗaukar ma'aikata daga mataki na ɗaya zuwa na Bakwai.

Wannan na zuwa ne biyo bayan zaman majalisar na ranar Litinin 2 ga watan Maris, 2026.

Kazalika majalisar ta kuma yi gyaran dokar ma'aikatan majalisar dokokin jihar Kano, inda ta amince da samar da mataimakin akawun majalisar na biyu.

Da yake ƙarin bayani, Shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Husaini Dala, ya ce baya ga ɗaukar ma'aikata hukumar za kuma ta rinƙa kula da tabbatar da tarbiyyar ma'aikata, da ladaftar da su, da sauya musu gurin aiki, da ciyar da su gaba, tare da basu horo, da sauran abubuwa na inganta aiki.

Wakilinmu Sunusi Shu'aibu Musa ya ruwaito cewa, Hon. Dala ya kuma ce, Hukumar za ta samu ne ƙarƙashin guda daga cikin ƙwararru a aiki, wanda ya ajiye aiki da matakin albashin sa bai gaza 15 ba, tare da samar da ƴan Hukumomi, a ƙarƙashin ta, da za su kasance a matsayin hukumar gudanarwar ta.

Ready to PlayDala FM88.5 FM