An rantsar da sabbin ƴan majalisar ƙananan hukumomin Ungogo da Birni a Kano

Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta rantsar da sabbin ‘yan majalisa masu wakiltar ƙananan hukumomin Birni Nabil Aliyu Daneji, da na Ungoggo Sa'ad Aminu Sa'adu.
Rantsuwar ta gudana ne a zaman majalisar na ranar Talata 3 ga watan Fabrairu, 2026, bisa jagorancin shugaban majalisar Hon. Jibril Isma'il Falgore.
Jim kaɗan bayan rantsuwar, sabbin ƴan majalisar sun bayyana cewa za su cigaba da ayyukan da iyayen su suka bari ka'in da na'in.
A yayin zaman majalisar na yau Talata, ta kuma karɓi ƙudurin ɗaga likkafar asibitin sha ka tafi na garin Gwarzo zuwa babban asibiti.
Ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Gwarzo, Yunusa Haruna Kayyu, ne ya gabatar da ƙudurin.
Wakilinmu na majalisar dokokin jihar Kano Sanusi Shu'aibu Musa ya ruwaito cewa, ɗan majalisar ya bayyana cewa asibitin na da matuƙar muhimmanci ganin yadda ya yi iyaka da ƙaramar hukumar Ƙaraye da ke jihar Kano.


