Koma Labarai
Labarai

Tauye Haƙƙi: Lauyoyin Gwamnatin Kano sun shirya tsunduma yajin aiki a jihar

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Tauye Haƙƙi: Lauyoyin Gwamnatin Kano sun shirya tsunduma yajin aiki a jihar

Lauyoyin Gwamnatin jihar Kano, na ma'aikatar Shari'a (Ministry of justice Kano State) sun shirya tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a faɗin jihar.

Shugaban ƙungiyar lauyoyin Barrister Abdullahi Aminu Shamsu, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Talata 10 ga watan Maris, 2026.

Barrister Shamsu ya bayyana cewar sun zartas da shawarar tafiya yajin aikin ne sakamakon rashin biyan su wasu haƙƙoƙinsu da gwamnatin ta ke yi.

A cewar sa, "Mun daɗe mu na faɗi tashi da shari'u musamman na manyan laifuka, da kuma barazana da mu ke fuskanta daga ƴan Shari'a amma duk da haka haƙƙin mu na lauya baya fita, in ji shi.”

Wakilinmu Yusif Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, Barrista Shamsu ya kuma bayyana cewar, tun a baya sun zauna da gwamnatin amma har zuwa yanzu haƙƙoƙinsu sun gaza fita a don haka suka zartas da shawarar tafiya yajin aikin.

Ready to PlayDala FM88.5 FM