An kulle ƙofar shiga kotun Noman'sland sakamakon yajin aikin lauyoyin gwamnatin Kano.
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Ƙungiyar lauyoyin gwamnatin jahar Kano, ta garƙame ƙofar shiga ma'aikatar shari'a, da wani ƙaton Mukulli sakamakon yajin aikin da lauyoyin suka fara da safiyar yau Laraba.
Lauyoyin gwamnatin dai sun tsunduma yajin aikin ne sakamakon rashin biyan su wasu haƙƙoƙinsu da suka ce doka ce ta tanadi a biya su.
Tuni dai Hukumar gudanarwa a ma'aikatar shari'a ta buƙaci lauyoyin da su fito aiki, harma ta yi barazanar ɗaukar matakin horo a kan duk wanda ya ƙi bin wannan umarnin.
Shima kwamishinan shari'ar na jihar Kano Barrister Abdulkarim Maude SAN, ya roƙi ƙungiyar lauyoyin da su yi wa mahukuntan Ma'aikatar hanzari, inda ya bayyana cewar suna aiki tuƙuru domin kyautata yanayin aiki cikin aminci da bin doka da oda.



