Koma Labarai
Labarai

Bikin Sallah: Gwamnan Sokoto ya amince da biyan ma'aikatan jihar albashin watan Maris, 2026.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Bikin Sallah: Gwamnan Sokoto ya amince da biyan ma'aikatan jihar albashin watan Maris, 2026.

Gwamnan Jihar Sokoto Ahmed Aliyu, ya amince da fara biyan albashin watan Maris ga ma’aikatan gwamnati kafin bukukuwan ƙaramar Sallah, da za a gudanar.

Hakan na cikin sanarwar da Daraktan Yaɗa Labaran Gwamnan Abubakar Bawa ya fitar a ranar Alhamis 12 ga Maris 2026.

Sanarwar ta kuma ce za a fara biyan albashin ne daga ranar Juma’a 13 ga Maris 2026 domin bai wa ma’aikata damar shiryawa bukukuwan Sallah cikin sauki.

Kafar yaɗa labarai ta Arewa updates ta ruwaito cewa, sanarwar ta ce biyan kudin zai shafi ma’aikatan gwamnatin jihar, ma’aikatan kananan hukumomi, ma’aikatan Hukumar Ilimin Kananan Hukumomi da kuma masu karɓar fansho a fadin jihar ta Sokoto.

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa gwamnan wanda ke kasar Saudiyya domin gudanar da Umrah ya bukaci ma’aikata su ci gaba da nuna kwarewa da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu.

Ready to PlayDala FM88.5 FM