Ƙungiyar KHZ Foundation ta baiwa iyayen marayu da masu buƙata ta musamman su 40 tallafin kuɗi a Kano

Ƙungiyar mu haɗa zumunci da ke rajin tallafa wa marayu da iyayensu da kuma masu bukata ta musamman ta KHZ Foundation, ta buƙaci gwamnati da masu hannu da shuni da su ƙara dagewa wajen tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi da masu buƙata ta musamman domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa.
Zaɓaɓɓen Daraktan ƙungiyar a nan Kano Baba Balarabe Kabir, ne ya bayyana hakan yayin taron tallafa wa marayu, da iyayen su, da kuma masu buƙata ta musamman da ta basu tallafi Naira dubu biyar biyar, yau a ɗakin taro na Balarabe Kabir da ke hukumar ƙidaya ta kasa da ke kan titin Ibrahim Dabo.
Baba Balarabe, ya kuma ce sun tallafa wa kimanin iyayen marayun da masu bukata ta musamman ɗin su 40, a wannan shekarar domin rage musu wani radadin rayuwa, duba da halin da ake ciki a yanzu.
Ya kuma buƙaci waɗanda suka rabauta da tallafin kuɗin da su yi abinda ya dace da abinda aka basu domin cin moriyar su tare da iyalansu.
A cewar sa, "Wasu lokutan ƙungiyar mu tana bayar da tallafin ɗanyen abinci, ko dafaffen abinci na shan ruwa a cikin unguwannin birnin Kano, tare da tallafa wa yara marayu, da ɗinkin Sallah, don taimaka wa rayuwar su, in ji Baba Balarabe.”
Ƙungiyar ta KHZ Foundation, ta kuma ce za ta ƙara ruɓanya ƙoƙarin ta wajen tallafa masu ƙaramin ƙarfi, da buƙata ta musamman, da ma matasa, domin ƙara inganta rayuwar su.



