NDLEA ta kama ƙwayoyin Pregabalin 75,000 da kwalaben Codeine 556 a Kano
0 views

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA, reshen jihar Kano, ta bayyana kama sama da ƙwayoyin da ke bugar wa nau'in Pregabalin 75,000, a jihar.
Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar a Kano, Sadek Muhammad Mai Gatari, ne ya bayyana hakan ta cikin sanarwar da ya fitar a ranar Litinin 16 ga Maris, 2026.
Sanarwar ta ce, an kuma kama kwalaben Codeine aƙalla guda 556, inda da aka shigo da su Kano, yayin da ake niyyar amfani da su yayin bikin ƙaramar sallar da ke gabato wa.
Mai Gatari, ya ce nasarar kama kayan mayen na zuwa ne a yayin sumamen da hukumar ke kai wa a wani ɓangare na Operation Ramadan Mubarak.



