Koma Labarai
Labarai

Ramadan: Ƙungiyar Tauraro ta tallafa wa marayu 50 da kayan Sallah a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Ramadan: Ƙungiyar Tauraro ta tallafa wa marayu 50 da kayan Sallah a Kano

Ƙungiyar tallafa wa marayu da masu ƙaramin ƙarfi ta Tauraro da ke garin Rafin Mallam a ƙaramar hukumar Ungogo a Kano, ta raba tallafin kayan sallah ga marayu 50 a yankin don rage musu raɗaɗin rayuwa.

Rabon tallafin ya gudana ne a ranar Litinin 16 ga Maris, 2026, a yankin garin Rafin Mallam, karo na 4, domin rage wa yara marayun wani raɗaɗin marayu halin ƙuncin rayuwar da suka samu kan su a ciki.

Da yake jawabi a yayin taron bada tallafin, shugaban ƙungiyar ta Tauraro Ibrahim Rabi'u Abdulƙadir, ya ce aƙalla marayu 50 ne suka rabauta da kayan sallar da kuma takalma, maza 22, yayin da mata suka kasance 27.

A cewar sa, "Babbar manufar mu na tallafa wa marayun shi ne domin suma su yi farin ciki a lokacin bikin sallar kamar wanda yake da iyaye, in ji shi.”

Ya ƙara da cewa bata ga batun tallafa wa marayu da kayan sallar, suna kuma ƙoƙarin samar musu sana'ar yi domin su taso suna dogaro da kan su ta ɓangarori daban-daban.

Ibrahim Rabi'u, ya kuma yi kira ga masu hali da su ƙara tashi tsaye domin shigo wa wajen tallafa wa marayu da masu ƙaramin ƙarfi ta yadda za a rage musu wani raɗaɗin rayuwa.

A yayin taron al'umma da dama ne na ciki da na wajen yankin suka samu damar halarta, inda marayu suka rinƙa bayyana farin cikin su bisa tagomashin da suka samu.

Ready to PlayDala FM88.5 FM