Koma Labarai
Labarai

Mai martaba Sarki Muhammad Sanusi II ne zai yi Hawan Sallah - Gwamnatin Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Mai martaba Sarki Muhammad Sanusi II ne zai yi Hawan Sallah - Gwamnatin Kano

Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta sanar da al’umma cewa ta samu sahihan bayanan sirri daga Majalisar Tsaro ta Jiha, da ke nuna cewa akwai wasu mutane da ke ƙoƙarin haddasa rikice-rikice da tayar da zaune tsaye a lokacin bukukuwan ƙaramar sallah (Eid-el-Fitr) da ke tafe.

Cikin sanarwar da Kwamishinan yaɗa labarai da al'amuran cikin gida na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar a yau, ya ce gwamnatin ta jaddada cewa duk da ƙoƙarinta na karewa da bunƙasa al’adun gargajiya na Kano, ba za ta lamunci duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma ba.

Sanarwar ta ce, bayan tattaunawa da Majalisar Masarautar Kano da sauran masu ruwa da tsaki, gwamnati ta amince da waɗannan tsare-tsare kamar haka;

Hawan Idi: Za a gudanar da shi karkashin jagorancin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II, daga filin Idi na Kofar Mata, ta hanyoyin da aka tsara, har zuwa Gidan Shettima, sannan a ƙare a Kofar Fatalwa ta Fadar Sarkin Kano.

Hawan Nasarawa: Za a gudanar da shi a wani salo na musamman, amma ba tare da hawa dawakai ba.

Hawan Daushe: An dakatar da shi a wannan lokaci, kuma za a mayar da shi zuwa wasu bukukuwan Sallah na gaba, in Allah ya yarda.

Kazalika an dakatar da Hawan Fanisau da Hawan Dorayi, na ɗan lokaci domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin jihar.

Gwamnatin ta kuma umarci dukkan hukumomin tsaro da su ƙara zage damtse wajen sa ido, tare da tabbatar da bin waɗannan umarni, da kuma ɗaukar duk matakan doka don hana duk wani tashin hankali kafin, lokacin, da bayan Sallah.

Haka kuma, gwamnati ta buƙaci al’umma da su kasance masu bin doka, su ba hukumomin tsaro haɗin kai, su guji yaɗa jita-jita, tare da gudanar da harkokinsu cikin lumana a duk lokacin bukukuwan Sallah.

Gwamnatin Jihar Kano ta kuma gode wa jami’an tsaro bisa jajircewarsu wajen tabbatar da zaman lafiya, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da aiki domin ganin an gudanar da bukukuwan cikin kwanciyar hankali.

A ƙarshe, gwamnatin Kano ta taya dukkan Musulmi murnar zagayowar Eid-el-Fitr, tare da fatan a yi Sallah lafiya.

Ready to PlayDala FM88.5 FM