Hukumar Road Safety ku ƙara jami'an ku don daƙile tuƙin gangancin Ƴan Kwanyo a Kano - Human Rights

Hukumar Road Safety ku ƙara jami'an ku don daƙile tuƙin gangancin Ƴan Kwanyo a Kano - Human Rights
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Center for Human Rights and Charity Development initiatives, ta yi kira ga Hukumar kiyaye aukuwar haɗura ta ƙasa reshen jihar Kano, da ta ƙara baza jami'an a titunan jihar domin daƙile haɗin da ke cikin gudun gangancin da wasu masu Babura da ake kira Ƴan Kwanyo ke haifar wa.
Shugaban gudanarwar ƙungiyar a matakin ƙasa Kwamared Tasi'u Idris Idris Soja, shi ne ya bayyana wa Dala FM Kano, hakan a yammacin ranar Lahadi 22 ga watan Maris, 2026.
Ya ce akwai buƙatar Hukumar kiyaye aukuwar haɗuran ta ƙara yawan jami'an ta a yankin Kabuga, bisa yadda Ƴan Kwanyon suke buge mutane sakamakon tuƙin gangancin da suke yi a yankin da ma wasu sassan jihar Kano.
Soja ya kuma ce, ko a yau sai da wasu masu Babura da ake kira Ƴan Kwanyo, suka buge kusan mutane biyar a yankin Kabuga, kuma suka gudu a yayin da suke guje-gujen su na fitar hankali, abinda ya tayar da hankalin jama'a a yankin.
A cewar sa, "Mu na yabawa jami'an hukumar bisa ƙoƙarin da suke yi wajen daƙile afkuwar haɗura, amma dai akwai buƙatar Hukumar ta ƙara dagewa wajen ganin an daƙile haɗarin da Ƴan Kwanyon ke haifar wa a yayin bikin ƙaramar sallar da ake ciki, in ji shi.”
Tasi'u Idris ya kuma yi kira ga iyaye da su gargaɗi ƴaƴansu wajen ganin sun tsawatar musu kan kaucewa gudun wuce sa'a a yayin da suke tuƙi da ababen hawa a yayin bukukuwan ƙaramar Sallar idin da ake yi, domin gujewa abinda ka je ya dawo.



