Koma Labarai
Labarai

Gwamnatin Tarayya da jihohi sun yi afuwa ga Fursunoni sama da 8,300

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Gwamnatin Tarayya da jihohi sun yi afuwa ga Fursunoni sama da 8,300

Gwamnatin Najeriya, tare da gwamnatocin jihohin ƙasar, sun amince da yafe wa (pardon) fursunoni sama da 8,300 a gidajen yari a faɗin Najeriya.

Kafar yaɗa labarai ta Mikiya ta ruwaito cewa, rahotanni sun nuna cewa matakin na daga cikin ƙoƙarin rage cunkoso a gidajen yari, da kuma bai wa wasu dama su koma cikin al’umma su fara sabuwar rayuwa.

Ana sa ran waɗanda suka ci gajiyar afuwar su haɗa da waɗanda suka aikata ƙananan laifuka, waɗanda suka nuna kyakkyawan hali a gidan yari, da kuma waɗanda suka kusa kammala zaman hukuncinsu.

Masana na cewa wannan mataki na iya taimakawa wajen gyaran halayya da rage cunkoso, amma yana buƙatar kyakkyawan shiri na sake haɗa su da al’umma (reintegration) domin hana su komawa laifi.

Ready to PlayDala FM88.5 FM