Koma Labarai
Labarai

An dakatar da Shugaban ƙaramar hukumar Kura da mataimakinsa na tsawon watanni uku

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
An dakatar da Shugaban ƙaramar hukumar Kura da mataimakinsa na tsawon watanni uku

Rahotanni daga ƙaramar hukumar Kura a Kano, na bayyana cewa kansilolin majalisar karamar hukumar sun yi wani zaman amincewa da dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Rabi'u Babina Ƙarfi.

Zaɓaɓɓen Mazaɓar Sarkin Kura, Hon. Tijjani Na Naba Kura, mai wakiltar Kura, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da manema labarai a yammacin ranar Juma'a 3 ga watan Afrilu, 2026.

Ya ce dakatarwar ta biyo bayan zarge-zargen badaƙalar wasu kuɗaɗe da suka kai kusan Naira miliyan ɗari biyu da hamsin, da ma zarge-zarge a kan badaƙalar filaye.

Ya kuma ce wannan na zuwa zuwa ne a dai-dai lokacin da mafi yawa daga cikin kansilolin ƙaramar hukumar suka amince da dakatarwar.

A cewar sa aƙalla Kansiloli 6 daga cikin 10, ne suka amince da dakatar da shugaban ƙaramar hukumar ta Kura Hon. Rabi'u Abubakar Babina, da mataimakin sa Hon. Bello Gambo Kura, na tsawon watanni uku, a kan badaƙalar kuɗaɗen.

Sai dai kuma shugaban masu rinjaye na kansilolin Hon. Yahuza Ashiru Zakariyya, mai wakiltar Mazaɓar Tanawa, na daga cikin waɗanda ba su sa hannu a kan takardar dakatarwar ba bisa dalilansa kamar haka.

Wakilinmu Ibrahim Abdullahi Soron Ɗinki ya ruwaito cewa, sai dai kawo yanzu dakataccen shugaban ƙaramar hukumar ta Kura, bai kai ga magantuwa ba amma da zarar ya magantu za a ji mu da shi.

Ready to PlayDala FM88.5 FM