An dawo da ƴan Najeriya 522 Kano, waɗanda suka maƙale a Jamhuriyar Nijar
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Rahotanni sun bayyana cewa ƴan Nijeriya 522 da suka makale a jamhuriyar Nijar, sun sauka a jihar Kano.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasar, NEMA ce ta karɓe su, a cikin shirinta na dawo da ƴan kasa.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, a cikin waɗanda suka dawo, akwai manyan maza 261 da kuma mata 101, sai matasa maza 82 da mata 72.



