Koma Labarai
Labarai

Gwamnatin Kano za ta kashe sama da biliyan huɗu na jarabawar sakandare ga ɗaliban jihar - Gwani Ali Makoɗa

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Gwamnatin Kano za ta kashe sama da biliyan huɗu na jarabawar sakandare ga ɗaliban jihar -  Gwani Ali Makoɗa

Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya biya wa ɗalibai sama da 153,141, da suka yi nasara a jarabawar Kwalafayin ƴan asalin jihar, kuɗin jarabawar Neco, domin taimaka wa ilimin su.

Kwamishinan Ma'aikatar Ilimi na jihar Kano, Gwani Dr. Ali Haruna Makoɗa, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da ya gudanar a ofishin sa, a ranar Lahadi 12 ga watan Afrilu, 2026.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne lokacin da yake bayyana sakin sakamakon jarrabawar Kwalafayin, na ɗalibai ƴan asalin jihar Kano, da suka zana a shekarar a shekarar 2025, ta wannan zangon da ake ciki.

Ya ce aƙalla ɗalibai dubu 163,457, ne suka zana jarabawar daga ɓanagren KERD, da Kimiyya da fasaha da kuma ɓangaren Arabiyya da Tahafiz, inda ɗalibai dubu 153,141, suka yi nasara a jarabawar, lamarin da aka samu maki kusan kashi 95.2 cikin waɗanda suka samu nasarar.

A cewar sa, "Ɗaliban ɓamgaren KERD 136,554, ne suka zana jarabawar ta Kwalafayin, inda ɗalibai ɗalibai 130,707, ne suka samu nasarar cin jarabawar, in ji shi.”

Kazalika, Makoɗa ya kuma ce a ɓanagren kimiyya akwai ɗalibai 3,0764, da suka zauna jarabawar, inda aƙalla ɗalibai 3,102, suka yi nasarar cin jarabawar, idan aka haɗa da na fasaha shi ne ya tasamma ɗalibai 7,442, da suka samu nasara.

A cewar sa, a ɓangaren ɗalibai masu karatun Islamiyya, da Tahafiz na Al-kur'ani mai girma, akwai ɗalibi dubu 18,414, da suka zauna jarabawar, inda ɗalibai 15,264, suka samu nasarar cin jarabawar.

Gwani Ali Haruna Makoɗa, ya ce idan aka haɗa dukkanin ɗaliban da suka yi nasara a jarabawar Kwalafayin ɗin ta shekarar 2025, sun tasamma dalibai 153,414, kuma sune Gwamnatin Kano ta ɗauki nauyin biya musu kuɗin jarabawar Neco, ga dukkan wanda ya samu maki biyar (Five Credit) ko da kuwa babu Turanci da Lissafi.

Dr. Makoɗa, ya kuma ce gwamnatin jihar Kano ta biya wa aƙalla ɗalibai 153,414, zunzurutun kuɗi Naira biliyan huɗu da miliyan ɗari huɗu da hamsin da Naira dubu ɗari biyar da hamsin da huɗu da ɗari bakwai, da za su zana jarabawar Neco.

Tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewa, Gwamnatin Kano ta kuma gargaɗi dukkanin shugabannin makarantun sakandare da su guji karɓar kuɗin ɗalibai a yayin karɓar sakamakon su, yana mai cewar duk wanda aka samu da laifin karɓar kuɗin ya kuka da kansa.

Ready to PlayDala FM88.5 FM