Koma Labarai
Iftila'i

Mataimakin Kakakin Majalisar dokokin jihar Nasarawa ya tsallake rijiya da baya

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Mataimakin Kakakin Majalisar dokokin jihar Nasarawa ya tsallake rijiya da baya

Rahotanni sun bayyana cewa Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa, Muhammad Adamu Oyanki, ya tsallake rijiya da baya bayan ya yi hatsarin mota a kan hanyar Keffi zuwa Akwanga a safiyar ranar Litinin 20 ga watan Afrilu, 2026.

Majiyoyin labarin sun bayyana cewa, hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na safe, inda daga bisani aka kwashe motarsa mai matuƙar lalacewa zuwa harabar majalisar da ke Lafia.

Kakakin majalisar, Danladi Jatau, tare da wasu ‘yan majalisa sun duba motar, inda ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, amma ya gode wa Allah da babu wanda ya rasa ransa.

A cewarsa, babban abin farin ciki shi ne yadda Mataimakin Kakakin ya tsira da ransa, domin rahotanni sun tabbatar da cewa yana cikin ƙoshin lafiya a halin yanzu.

Ready to PlayDala FM88.5 FM