Koma Labarai
Wasanni

Jihar Kano ta samu tikitin buga gasar wasanni ta ƙasa NSF na 2026, a Enugu.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Jihar Kano ta samu tikitin buga gasar wasanni ta ƙasa NSF na 2026, a Enugu.

Jihar Kano ta samu tikitin buga gasar wasanni ta ƙasa, wato National Sport Festival 2026, a jihar Enugu.

Wannan na cikin wata sanarwa da ‎Jami’in yaɗa labarai na hukumar wasanni ta Kano Ashiru Rabiu Gidan Tudu ya sanyawa hannu.

Sanarwar ta ce jihar Kano ta samu tikitin shiga gasar wasanni ta ƙasa ta 23rd National Sports Festival 2026 a dukkan wasannin da ta fafata.

‎Da yake bayyana farin cikinsa kan wannan nasara, Shugaban Hukumar Wasanni ta Kano, Alhaji Muhammad Tukur Babangida, ya gode wa Allah bisa wannan babban ci gaba da jihar ta samu.

‎Ya yabawa ‘yan wasa, da masu horaswa, da kuma jami’an Hukumar Wasanni, da dukkan waɗanda suka bayar da gudunmawa wajen ganin an samu nasarar.

Gasar wasanni ta kasa ta wannan shekarar dai za ta gudana ne a jihar Enugu.

Ready to PlayDala FM88.5 FM