Shugabar Ma'aikatan Gwamnatin Kano, ta duba wuraren wasanni gabanin gasar PEPSGA.

Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Kano, Hajiya Bilkisu Shehu Maimota, ta jagoranci duba wasu manyan filayen wasanni a faɗin Jihar a yau Litinin, a wani ɓangare na shirye-shiryen karɓar baƙuncin Gasar Ma’aikatan Gwamnati, (Federation of Public Service Games).
Dala FM Kano ta ruwaito cewa, wannan na cikin wata sanarwa da Daraktar wayar da kan jama'a ta Ofishin shin Shugabar Ma'aikatan Gwamnatin, Ruƙayya Uba Sulaiman ta fitar a ranar Litinin 21 ga watan Satumba, 2026.
Sanarwar ta ce, manufar ziyarar ita ce tantance shirye-shiryen wuraren wasannin da kuma tabbatar da cewa sun dace da ƙa’idojin da ake buƙata domin gudanar da gasar cikin nasara.
Shugabar Ma’aikatan ta kasance tare da Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano, Alhaji Muhammad Tukur Babangida, manyan Sakatarorin gwamnati da suka haɗa da Sabi'u Shu'aibu na ma'aikatar ayyuka na Musamman, da Abba A. Danguguwa mai kula da ma’aikatar ma’aikata, da sauran manyan jami’an gwamnati ciki har da masu kula da harkokin matasa da wasanni.
Wuraren da aka ziyarta sun haɗar da Kano Club, Kwalejin Sa’adatu Rimi da Jami’ar Bayero ta jihar Kano, da sauran wurare.
A yayin ziyarar, Hajiya Bilkisu Shehu Maimota ta jaddada muhimmancin kyakkyawan shiri, haɗin kai da kuma tabbatar da samar da dukkan abubuwan da ake buƙata, domin bai wa ƴan wasa da jami’an gasar kyakkyawan yanayi.
Ta bayyana kwarin gwiwar cewa, ta hanyar haɗin kan dukkan masu ruwa da tsaki, Jihar Kano za ta yi nasarar karɓar bakuncin gasar "Federation of Public Service Games" tare da samun nasara.


