Koma Labarai
Wasanni

An gayyaci wakilan Kano na Para Taekwondo zuwa sansanin Najeriya bayan nasarar da suka samu.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
An gayyaci wakilan Kano na Para Taekwondo zuwa sansanin Najeriya bayan nasarar da suka samu.

Hukumar Wasanni ta Kano ta bayyana cewa wakilan jihar a bangaren wasan Para Taekwondo, sun samu nasara a gasar Korean Ambassador Taekwondo Championship 2026, wadda Ofishin Jakadancin Koriya da ke Najeriya ke shiryawa a duk shekara.

Wannan na cikin sanarwar da jami'in yaɗa labarai na hukumar wasanni ta jihar Kano, Ashiru Rabi'u Gidan Tudu ya aikowa Dala FM Kano, a ranar Juma'a 23 ga watan Oktoba, 2026.

Sanarwar ta ce, a yayin gasar, Abdullahi Muhammad Lubiya mai nauyin kilo 65 ya lashe lambar zinare, yayin da Musa Bala mai nauyin kilo 56 ya samu lambar tagulla, bayan sun nuna bajinta a fafatawar da suka yi.

Sanarwar ta kuma ce, bayan wannan gagarumar nasara, an gayyaci ‘yan wasan biyu zuwa sansanin ƙasa Najeriya, domin ci gaba da shirye-shirye gabanin wakiltar ƙasar a babbar gasar Para Taekwondo da Koriya za ta karɓi baƙunci.

Da yake tsokaci kan nasarar, Sakataren Ƙungiyar Taekwondo ta Jihar Kano, Hafizu Usman, ya ce wannan ci gaba ya samu ne sakamakon kulawa, goyon baya da ƙarfafawar da yan wasan ke samu daga shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano, Alhaji Muhammad Tukur Babangida.

Hafizu Usman ya ce, irin wannan tallafi da kyakkyawan tsarin jagoranci na taimakawa wajen bunƙasa wasanni da kuma bai wa ƴan wasa damar nuna bajintar su a manyan gasanni.

Sanarwar ta ce, Hukumar Wasanni ta Jihar Kano ta taya ‘yan wasan murna, tare da yaba wa masu horaswa da jami’an ƙungiyar bisa irin ƙoƙarin da suke yi wajen ɗaukaka martabar Kano a fagen wasanni.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM