Iran ta musanta jita-jitar sulhu tsakanin ta da Amurka

Gwamnatin juyin juya halin addinin musulunci a Iran ta musanta jita-jitar cewar tana neman komawa teburin sulhu da Amurka.
Iran ta nanata aniyar ta na ci gaba da aiwatar da hare-harenta kan manufofin Amurka a yankin na gabas ta tsakiya don fansar hare-haren da aka kai mata duk da makokin kwanaki 40 da ta fara don jimama mutuwar Ayatollahi Ali Khamne'i.
Hakan na zuwa ne yayin da aka shiga ƙwana na uku a jere da faro yaƙin, inda ma’aikatar tsaron Amruka Pentagon ta ce dakarun kasar uku sun gamu da ajalinsu, wasu biyar kuma sun samu munanan raunuka a hare-haren makami mai linzami da Iran ta kai kan sansaninta na Centcom a Gabas ta Tsakiya.
A nata bangare rundunar sojin Isra’ila ta ce ta yi nasara kashe manyan kwamandojin sojin Iran akalla 40, waɗanda suka haɗa da ministan cikin gidan ƙasar, da shugaban rundunar dakarun juyin juya halin ƙasar, ba yaga jagoran addini muslunci AyatollAh Ali Khamenei, da shi ma ya rasa ransa a farmakin.
A matsayin martani, dakarun rundunar kundun bala Kasar Iran IGRC ta harba makamai masu linzami a sassan Biranen Tel aviv, da Jérusalem, da ma wasu sansanonin sojin Amurka da ke Gabas ta Tsakiya.
Kafar BBC ta ruwaito cewa, ƙungiyar agaji ta Red Cross ta shaida mutuwar mutane 9 yayin da wasu 11 suka ɓata a lardin Bet Shemesh na Isra’ila, sakamakon hare-haren Iran.
Har ila yau, jaridu a yankin sun ruwaito cewa aƙalla mutane huɗu sun mutu yayin da wasu 58 suka jikkata bayan da Iran tayi ruwan makamai masu linzami kan biranen Doha, da Bahreïn da kuma Oman.
