Koma Labarai
Ƙetare

Hakan na zuwa biyo bayan kashe jagoran juyin juya hali na Iran Ayatullah Ali Khamene'i

0 views
Hakan na zuwa biyo bayan kashe jagoran juyin juya hali na Iran Ayatullah Ali Khamene'i

Kafofin yaɗa labarai a Iran sun ruwaito cewa, jagororin Iran na riƙon ƙwarya a Iran sun gudanar da zama a karon farko domin tattauna wa a kan batutuwan ƙasar.

Kafofin sun sanar da hakan ne a wani hoto da suka fitar,, sai dai babu cikakken bayani kan wuri da lokacin da aka gudanar da taron, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta BBC Hausa ta ruwaito.

Shugaban Iran Masoud Pezhakian, da babban alƙalin ƙasar Gholamhossein Mohseni-Ejei, da babban faƙihi Alireza Arafi ne suka halarci zaman.

Rahotanni sun bayyana cewa jagororin dai su ne za su cigaba da jagorantar harkokin addinin ƙasar har zuwa lokacin da za a naɗa sabon jagoran addini a ƙasar.

Ready to PlayDala FM88.5 FM