Harin jirage marasa matuƙar ya haifar da tashin wuta a matatar man ƙasar Saudiyya

Yanzu haka Hukumomin Saudiyya sun tabbatar da harin jirage marasa matuƙa kan matatan manta, ko da dai ƙasar ta ce ta samu nasarar daƙile wutar da ta tashi a matatar bayan kakkaɓo jiragen marasa matuƙa.
Cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labaran ƙasar ya wallafa, ya ce wutar ta yi wa matatar ''ƙaramar illa saboda ɓaraguzan'' jiragen da aka kakkaɓo sun faɗa wasu wurare.
Kazalika, Ma'aikatar makamashin ƙasar, ta ce an samu nasarar kashe wutar da ta matatar mai ta Ras Tanura - wanda kamfanin man ƙasar Aramco ke gudanarwa, yana mai cewa jami'an kashe gobara sun samu nasarar gaggauta kashe wutar.
Rahotanni sun bayyana cewa wani bidiyo da BBC ta tantance ya nuna yadda hayaƙi ya turnuƙe a saman matatar man ta Saudiyya.
Ƙasar dai ta daɗe tana bai wa dakarun Amurka da na ƙasashen Yamma mafaka Saudiyya, kuma a ranar Asabar gwamnatin ƙasar ta fitar da sanarwar Allah wadai kan hare-haren Iran.

