Zargin kashe jariri: kotu ta yi umarnin a tsare mai jego a gidan gyaran hali a Kano
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Kotun majistret mai lamba 9 ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Haulatu Magaji Kankarofi, ta aike da wata Mai jego, gidan ajiya da gyaran hali.
Matar mai suna Jummai Ahmad ana zargin ta da laifin haɗa baki da mahaifiyar ta da kuma laifin kashe jaririn da ta haifa.
Ƙunshi zargin ya bayyana cewar mai unguwar Gama E ne ya shigar da ƙarar wajen yansanda, inda su kuma bayan kammala bincike suka gurfanar da ita a kotun.
Ana kuma zargin Jummai ta haihu duk da cewar bata da miji a halin yanzu.
Sai dai tuni wadda ake zargi ta biyu mahaifiyar jummai ta tsere.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya ruwaito cewa laifukan sun saɓa da sashi na 97 da na 221 na kundin penal code.



