Koma Labarai
Shari'a

Kotu ta fara sauraren shaidun kariya kan wani matashi da ake zargi da kashe wata mata ta hanyar jefa ta cikin rijiya a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Kotu ta fara sauraren shaidun kariya kan wani matashi da ake zargi da kashe wata mata ta hanyar jefa ta cikin rijiya a Kano

Babbar Kotun jihar Kano, da ke zamanta a Bompai, ƙarƙashin jagorancin mai shari'a A'isha Mahmud, ta ci gaba da sauraron wata Shari'a wadda gwamnatin jaha ta shigar, tana ƙarar wani matashi mai suna Naziru Magaji Yalwar ɗan ziyal.

Ana zargin matashin ne da laifin kashe wata mata wadda ƙunshin zargin ya bayyana cewar ya jefa matar a rijiya daga nan ta rasa ranta.

A zaman kotun na ranar Alhamis 2 ga Yuli, 2026, wanda ake tuhumar ya fara kare kansa, inda ya bayyana wa kotun cewar lokacin da aka jefa matar a rijiya ta mutu shi ba ma ya garin Tofa ya na yalwar ɗan ziyal.

Shima malamin matashin ya bayyana cewar, su na tare a tsangaya suka samu labarin rasuwar matar.

Wakilinmu na Kotu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, kotun ta ɗage sauraron shari'ar zuwa ranar 27 ga watan gobe domin ci gaba.

Ready to PlayDala FM88.5 FM