Gwamnan Kano ya taya shugaban Najeriya, Tinubu murnar cika shekaru 74

Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya taya Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, murnar cika shekara 74 da haihuwa.
Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu a ranar Asabar 28 ga watan Maris, 2026.
A madadin gwamnati da al’ummar Jihar Kano, Gwamna Yusuf ya bayyana ranar haihuwar shugaban ƙasar a matsayin wata dama ta nuna girmamawa ga jagoranci, jajircewa da sadaukarwar da yake yi wajen hidimtawa ƙasa.
Gwamnan ya yabawa Shugaba Tinubu bisa hangen nesansa da ƙoƙarinsa na ƙarfafa haɗin kai, zaman lafiya da bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.
A cewar sa, manufar gwamnatin Tinunu ta “Renewed Hope Agenda” na ci gaba da ƙara wa ‘yan Najeriya kwarin gwiwa.
Gwamna Yusuf ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da ya ba shugaban ƙasar lafiya, hikima da ƙarfi domin ci gaba da jagorantar harkokin ƙasa yadda ya kamata.
Haka kuma ya yi addu’ar Allah ya ba shi jagoranci da goyon baya wajen samar da ƙarin ribar dimokuraɗiyya ga ‘yan Najeriya.
Gwamnan ya sake jaddada cewa gwamnatin Jihar Kano za ta ci gaba da bai wa gwamnatin tarayya goyon baya da haɗin kai domin ciyar da ƙasa gaba, bisa tsarin “Renewed Hope Agenda” da kuma manufar “Kano First Agenda.”



