Mai baiwa Gwamnan Kano shawara kan tsaro ya yi murabus daga mukaminsa

Rahotanni sun bayyana cewa, Air Commodore (mai ritaya) Salisu Abdullahi Yusha’u Soja ya ajiye mukaminsa na mai bai wa Gwamnan Jihar Kano shawara kan harkokin tsaro (SA Joint Security Services), a jihar.
Cikin wasiƙar murabus ɗin da ya aike wa Gwamna Abba Kabir Yusuf, mai ɗauke da kwanan watan 26 ga Maris, 2026, Yusha’u ya bayyana cewa murabus ɗin nasa zai fara aiki ne daga ranar 30 ga Maris, 2026, da ake ciki.
Soja ya ce matakin da ya ɗauka ya biyo bayan umarnin da ya shafi sabuwar dokar zaɓe ta 2026, wadda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ita.
Dokar dai ta buƙaci duk masu riƙe da muƙaman gwamnati da ke da burin tsayawa takara su sauka daga mukamansu, nan da 31 ga watan Maris, 2026.
Tsohon jami’in sojan saman ya kuma gode wa gwamnan bisa damar da aka ba shi na yi wa al’umma hidima, tare da jaddada ci gaba da biyayya da kuma yi wa gwamnati fatan alheri.
Rahotanni na bayyana cewa, dan siyasar na shirin tsayawa takarar Ɗan majalisar tarayya a mazabar Tudun Wada da Doguwa, inda zai kalubalanci Hon. Alhassan Ado Doguwa, a zaɓen 2027, kamar yadda kafar Daily Nigerian Hausa ta ruwaito.



