Gwamnan Kano ya umarci jami'an gwamnati da ke son tsayawa takara a zaɓen 2027, su ajiye muƙaman su

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci dukkanin masu sha'awar tsayawa takara a jihar da su sauka daga muƙaman su, domin bin tanadin dokar zaɓe.
Hakan na cikin wata sanarwa da babban daraktan yaɗa labaran gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, inda ya ce umarnin ya fito ne ta hannun Sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Umar Farouk Ibrahim.
Sanarwar ta jaddada cewa matakin ya yi dai-dai da sashe na 88 ƙaramin layi na 1, na dokar zaɓe ta 2026, wanda ya ƙayyade yadda jami’an gwamnati ke shiga harkokin siyasa.
Sanarwar ta kuma ce Sakataren gwamnatin na cewa, an ɗauki wannan matakin ne domin tabbatar da adalci, gaskiya da kuma samar da damar fafatawa ga dukkan masu neman muƙamai.
Har ila yau, sanarwar ta umarci dukkan masu ruwa da tsakin da abun ya shafa, da su tabbatar da bin umarnin, inda aka buƙaci masu niyyar tsayawa takarar su yi murabus kafin ranar 31 ga Maris, 2026, da ake ciki.



