Koma Labarai
Siyasa

Hardwoker ya rushe Majalisar Zartarwar Ƙaramar Hukumar Kumbotso nan ta ke

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Hardwoker ya rushe Majalisar Zartarwar Ƙaramar Hukumar Kumbotso nan ta ke

Shugaban Ƙaramar hukumar Kumbotso Hon. Ali Musa Ɗanmaliki (Hardworker) ya rushe Majalisar Zartarwar Karamar hukumar Kumbotso, da ke Kano.

Shugaban ya sanar da hakan ne jim kadan bayan wata ganawa da yayi da daukacin Ma'aikatan karamar hukumar, tare da Shugaban kansiloli da dukkan zababbun kansilolin yankin, a ranar Litinin 30 ga watan Maris, 2026.

Daga cikin waɗanda aka rushe sun haɗar da dukkan Kansiloli masu Ofis, (Supervisory Councillors)da da dukkan masu baiwa shugaban ƙaramar hukumar shawara (special Advisors) nan take.

A cewar sa, "An ɗauki wannan mataki ne domin yin gyara tare da ƙara inganta harkokin aiki don damawa da kowane ɓangare na ƙaramar hukumar, in ji shi.”

Ready to PlayDala FM88.5 FM