Gwamnan Borno ya sauke kwamishinonin sa nan take
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Rahotanni sun bayyana cewa Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya rusa majalisar zartarwa ta jihar nan take.
Wannan na cikin sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jihar Borno Bukar Tijani ya fitar a ranar Litinin 30 ga Maris 2026.
Sanarwar ta ce wannan maataki zai bai wa duk wani mamba na majalisar damar shiga takarar a babban zaɓen da ke tafe na shekarar 2027.
Kazalika, Gwamnan ya kuma umarci dukkan kwamishinonin da aka sauke da su miƙa ragamar ma’aikatunsu ga manyan sakatarorinsu kafin ranar Juma’a 3 ga Afrilu 2026.



